logo

HAUSA

IOM ta bukaci taimakon gaggawa ko da za a kara samun ambaliyar ruwa a yankin Kahon Afirka

2023-06-29 10:03:26 CMG Hausa

A jiya ne, hukumar kula da ’yan gudun hijira ta duniya (IOM) a takaice, ta yi kira ga masu hannu da shuni, da ku kara samar da taimakon gaggawa don kara karfin juriya da kimtsawa karin ambaliyar ruwa da ake sa ran samu nan gaba a wannan shekara, sakamakon matsalar sauyin yanayi na El Nino.

A cikin rahotonta na baya-bayan nan game da matsalar fari da ta fitar a ranar Laraba, hukumar ta ce ta kara daukar matakan tunkarar matsalar fari a yankin gabashin Afirka, inda ta taimakawa sama da mutane miliyan 4.3 a kasashen Somaliya da Habasha tun daga watan Janairun 2022.

A cewar hukumar, yayin da aka kawar da yunwa ta hanyar zage damtse da bayar da taimako, akwai bukatar karin taimako daga bangarori daban daban da ma tallafin gaggawa, ciki har da sake gina tsarin yanayi na rayuwa, da karfafa juriya da kara shiryawa ambaliyar ruwa da ake sa ran samu nan gaba a wannan shekara, sakamakon aukuwar yanayi na El Nino. (Ibrahim)