logo

HAUSA

Al’ummar musulmin Nijar suka murnar bikin sallar layya

2023-06-29 10:05:48 CMG Hausa

Kamar sauren kasashen duniya, al’ummar musulmin kasar Nijar ba su tsaya baya ba wajen sallar layyar ranar jiya 28 ga watan Yunin shekarar 2023, inda babban masallancin Kadhafi da ke birnin Yamai ya karbi sallar Idi. Kuma shugaban kasa Mohamed Bazoum da mambobin gwamnati da sauran jakadun kasashe musulmi suka halarci wannan sallar Idi. 

Daga Yamai, abokin aikin mu Mamane Ada ya halarci wata sallar Idi a wani masallacin unguwar filin jirgi ga kuma rahoton da ya aiko mana jiya. 

Tun wajen karfe bakwai ne na safiyar ranar yau al’ummar musulmi maza da mata, yaro da babba, da ma tsoffafi cikin sabbin tufafi suka fara kwarara babban masallacin unguwar filin jirgi cewa da Aeroport domin samun damar gudanar da sallar Idi. Bayan kara raka’a biyu na sallar idin ya samu jin tabakin babban limamin da ya jagoranci sallar idin ya fara da gabatar da sunansa…

Assalam Alaikum wata alla wabaratu, suna Habibou Aboubacar Rabiou a nan Yamai a jamhuriyar Nijar a unguwar Aéroport masallaci na Juma’a na route Tchanga wanda ana juma’a kuma ana tamsiri kuma ana Idi a cikinsa. Huduba abin da ta kunsa daga cikin hudubobi na Idi a yau shi ne irin yadda manzon Allah SAW ya yi umurni wajen huduba yadda ya zo cikin kissoshi na Alkur’ani…Allah ya yarda kenan muna iyar ci daga cikinta kuma mu taimawa miskinai, mu ba da sadaka, mu ba da a layya duk ta yarda. 

Malam kun tabo zaman lafiya a cikin addu’o’in naku shin me ya sa ?

Saboda zaman lafiya shi ne babban ginshiki, idan babu zaman lafiya kai ba ka isa ka zo ka tsaya a wannan wuri ba, ka yi mini tambayoyi, ko ina dan adam bai kamata ya manta da zaman lafiya ba, zaman lafiya wani abu ne mai girma ga tarihin rayuwar dan adam, al’amu ana bukatar shi a kowane lokaci.

Akwai wani sako na musammun ga musulmi a wannan salla ta layya ?

Sakon da muke kira ga musulmi a wannan sallah ta layya shi ne kullum mu yi kokarin hada kanmu. Idan ka duba sallar Ramadan da ta wuce kusan duniya gaba daya, an yi shekaru aru aru wadanda ba a samu sallah rana guda ba irin ta Ramadan, kuma haka wannan sallah Alhamdu Lillahi, idan ana hadin kai kullum to ana samun ci gaba. Larabawa na cewa al’ittahadu kuwa, amma idan kuka rabu fatalshalu wata zaha ribakum haka Allah ya ce a cikin Alkur’ani, ke nan muna kira kan a hada juna, mu zama uwa daya uba daya kamar yadda shi manzon Allah SAW ma’ana ya yi kira. 

To bayan wannan sallar idi da yanke rago na limamin masallacin idi, sai sauran al’ummar musulmi suka shiga yanke nasu ragona da shirye-shiryen gashi da ayyukan za su kwashe tsawon yinin wannan ranar sallah, a yayin da su kama a daya bangare yara za su je yawon barka da sallah wajen ’yan uwa da abokan arziki kuma na hiranta da wasu daga cikinsu ina da suka bayyana fatan alheri da barka da sallah cikin annashuwa da jin dadi.

(Muryoyin wasu yara)

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.