logo

HAUSA

Rundunar RSF ta Sudan ta sanar da sakin fursinonin yaki 100

2023-06-28 10:06:55 CMG Hausa

Rundunar ko ta kwana ta Sudan ko RSF a takaice, ta sanar da sakin wasu sojojin fursinonin yaki su 100 a jajiberin ranar babbar sallah, duk da ci gaba da dauki ba dadin da ake yi tsakanin rundunar da sojojin gwamnati a birnin Khartoum.

RSF ta ce ta saki sojojin ne albarkashin bikin babbar sallah da al’ummar musulmi za su gudanarwa, tare kuma da la’akari da manufar jin kai.

Kafin hakan a ranar Litinin, kwamandan rundunar ta RSF Mohamed Hamdan Dagalo, ya sanar da tsagaita wuta na kwanaki 2, domin baiwa al’ummar musulmin kasar damar gudanar da bukukuwan sallah lami lafiya, ko da yake tsagin sojojin gwamnatin kasar ba su ce komai ba don gane da hakan.

Tun daga ranar 15 ga watan Afirilu ne dai Sudan ta tsunduma cikin yaki, tsakanin sassan biyu da ba sa ga maciji da juna, lamarin da ya rutsa da dubban ’yan kasar mazauna birnin Khartoum, fadar mulkin kasar da ma wasu karin yankunan kasar.

Alkaluman ma’aikatar lafiya ta kasar sun nuna cewa, kawo yanzu yakin ya sabbaba rasuwar sama da mutane 3,000, tare da jikkata sama da mutane 6,000.  (Saminu Alhassan)