logo

HAUSA

Saudiyya : sama da mahajjata miliyan 1.8 ne suka yi aikin Hajji a shekarar 2023

2023-06-28 10:41:46 CMG Hausa

 

A jiya Talata ne, Ministan Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya Tawfiq al-Rabiah ya sanar da cewa, mahajjata sama da miliyan 1.8 daga kasashe sama da 150 ne ke gudanar da aikin Hajjin bana.

Adadin mahajjata daga kasashen Larabawa ya zarta 346,000, kwatankwacin kashi 21 cikin kashi 100 na jimillar alhazai, in ji babbar hukumar kididdiga ta kasar a jiya Talata.

Daga cikin mahajjatan, akwai sama da miliyan 1 daga kasashen Asiya ban da kasashen Larabawa, wanda ke da kashi 63.5 cikin kashi 100 na jimillar alhazai, yayin da kusan mahajjata 223,000, wato kashi 13.4 cikin kashi 100, suka fito ne daga kasashen Afirka ban da kasashen Larabawa.

Mahajjata sama da 36,500 ne suka yi balaguro daga kasashen Turai da Amurka da Australiya da sauran kasashen da ba a lissafa ba zuwa kasar Saudiyya, wanda ke wakiltar kaso 2.1 na jimillar adadin, a cewar hukumar. 

A kasar Najeriya akwai alhazai dubu 95 da suka samu halartar aikin hajjin na bana.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.(Yahaya, Garba)