logo

HAUSA

Hukumar zaben Saliyo ta ayyana shugaban kasa mai ci Bio ya lashe zaben kasar karo na biyu

2023-06-28 10:54:32 CMG Hausa

 

A jiya Talata ne, hukumar zaben kasar Saliyo ta bayyana cewa, Julius Maada Bio, shugaban kasar mai ci kuma dan takarar jam'iyyar Saliyo mai mulki wato jam’iyyar Sierra Leone People's Party ya lashe wa'adin aikinsa na biyu na shekaru biyar a zaben shugaban kasar na bana.

A yayin taron manema labarai, hukumar zaben kasar Saliyo ta sanar da cewa, Bio ya samu kusan kaso 56.17 na yawan kuri'un da aka kada, yayin da dan takarar jam'iyyar adawa ta All People's Congress Samura Kamara ya samu kusan kaso 41.16 na yawan kuri’un.

A bisa doka a kasar ta yammacin Afirka, kafin a bayyana wani a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa, dole ne dan takarar da ke kan gaba ya samu kaso 55 na kuri'un da aka kada.

Saliyo ta gudanar da zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki da na kananan hukumomi a ranar 24 ga watan Yuni. (Yahaya)