logo

HAUSA

Jakadan Sin a Nijar ya halarci bikin bayar da gudummawar ragunan layya ga ’yan Nijar da bala'i ya rutsa da su

2023-06-27 13:59:18 CMG Hausa

Jakadan kasar Sin a jamhuriyar Nijar Jiang Feng, da ministan ayyukan jin kai da bala'o'i na Nijar Magaji Laouan, sun jagoranci bikin bayar da gudummawar raguna ga wadanda bala'in ya shafa a kauyen Dagu dake yankin Tillabery a Jamhuriyar Nijar. Dagacin kauyen Malam Harouna, da mazauna kauyuka fiye da 100 ne suka halarci bikin.

Jakada Jiang ya bayyana a yayin jawabin da ya gabatar cewa, ko da yake akwai nisan dubban mila-milai a tsakanin kasashen Sin da Nijar, al'ummomin kasashen biyu na da kyakkyawan zumunci a tsakaninsu.

Sallar Layya na daya daga cikin muhimman bukukuwa a Jamhuriyar Nijar. Wannan ya sa a wannan karo, ofishin jakadancin kasar Sin dake Nijar ya ba da gudummawar raguna 60 ga mazauna kauyen dake da karamin karfi, da nufin isar da sahihanci da abokantaka na jama'ar kasar Sin ga jama'ar Nijar. Matakin da ake fatan zai sanya farin ciki a zukatan iyalan dake fama da matsin rayuwa a lokacin bikin Sallah.

A nasa jawabin minista Laoun Magaji ya nuna cewa, kasashen Nijar da Sin ’yan uwan juna ne. Ya kuma nuna godiya da irin taimakon da ofishin jakadancin Sin da ke Nijar ya dade yana bayarwa. Ya ce, alherin da bangaren kasar Sin ya samar, zai baiwa iyalai masu karamin karfi da dama na jamhuriyar Nijar damar yin bikin babbar Sallah cikin mutunci, kuma al'ummar Nijar za su rika tunawa da shi a cikin zukatansu. (Ibrahim Yaya)