logo

HAUSA

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya yi tsokaci kan lamarin kungiyar Wagner

2023-06-26 11:09:29 CMG Hausa

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a ranar Lahadin da ta gabata cewa, kasar Sin tana goyon bayan kasar Rasha wajen kiyaye zaman lafiyar kasa da samun ci gaba da wadata.

A cewar rahotanni, Yevgeny Prigozhin, wanda ya kafa kungiyar Wagner, da dukkan dakarun Wagner sun janye daga hedkwatar cibiyar sojojin kudancin Rasha.

Prigozhin ya amince da shawarar shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko na kungiyar ta dakatar da ayyukanta na soja a kasar Rasha tare da daukar karin matakai na sassauta tashin hankali. Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ba da tabbacinsa cewa Prigozhin na iya zuwa Belarus kuma Rasha za ta yi watsi da tuhumar da ake masa.

Da yake amsa tambayar manema labarai, kakakin ya ce lamarin da ya faru tsakanin dakarun Wagner da kasar lamari ne na cikin gidar Rasha.

Kakakin ya kara da cewa, a matsayinta na makwabciyar kwarai ta kasar Rasha, kuma babbar abokiyar huldar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare na sabon zamani, kasar Sin tana goyon bayan kasar Rasha wajen kiyaye zaman lafiyar kasa da samun ci gaba da wadata. (Yahaya Yahaya)