logo

HAUSA

Putin ya ba da umarnin kawar da wadanda suka shirya tawaye na Wagner

2023-06-24 20:40:39 CMG Hausa

A yau Asabar ne shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa, ya baiwa sojojin kasar Rasha umarnin da ya dace na dakile dakarun da suka shirya tawaye na kungiyar soji masu zaman kansu ta Wagner.

Shugaban Wagner Yevgeny Prigozhin a nasa bangaren ya yi watsi da zargin Putin na cewa shi “maci amanar kasa” ne, yana mai cewa dakarun kungiyar sojin masu zaman kansu “'yan kishin kasa ne”.

Prigozhin ya zargi sojojin Rasha da kai wani mummunan hari da makami mai linzami kan dakarunsa a ranar Juma'a, ikirarin da ma'aikatar tsaron Rasha ta musanta.

An tsaurara matakan tsaro a birnin Moscow da wasu yankuna na kasar Rasha a daidai lokacin da al'amura ke kara ta'azzara. (Yahaya)