logo

HAUSA

Rasha ta bude shari'a a kan shugaban Wagner kan tada zaune tsaye

2023-06-24 16:57:59 CMG Hausa

Kafafen yada labaran Rasha sun labarta a ranar Jumma’a kamar yadda suka nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na hukumar yaki da ta’addanci ta kasar Rasha cewa, jami’an tsaron FSB na kasar Rasha sun bude shari’a kan Yevgeny Prigozhin, shugaban kungiyar soji mai zaman kanta ta Wagner na kasar Rasha, bisa yin kira da a yi tashe-tashen hankula.  

A ranar Juma'ar ne Prigozhin ya zargi sojojin Rasha da "halaka" mayakansa, ba tare da bayyana cikakken bayanin zarginsa ba, ya kuma sha alwashin dakatar da abin da ya kira "mugunta" na shugabancin sojojin.

Ma'aikatar tsaron Rasha ta musanta rahotannin da ke yawo a shafukan sada zumunta na cewa sojojin kasar sun kai hare-hare kan sansanonin Wagner tare da yin kira ga mayakan Wagner da su "dakatar da ginshikan" su koma bakin aikinsu.

An tsaurara matakan tsaro a birnin Moscow da kuma birnin Rostov da ke kusa da kudu maso gabashin Ukraine, kamar yadda kafafen yada labaran kasar Rasha suka rawaito a safiyar yau Asabar.

Babban mai gabatar da kara na kasar Rasha Igor Krasnov ya sanar da shugaban kasar Vladimir Putin game da laifin da ake tuhumar Prigozhin da shi, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na TASS ya rawaito daga bakin kakakin Kremlin Dmitry Peskov. Ya kara da cewa manyan jami'an Rasha na FSB da ma'aikatar tsaro da ta cikin gida suna ba da rahoto ga Putin kan matakan da suke dauka don mayar da martani ga tada zaune tsayen. (Yahaya)