logo

HAUSA

An kaddamar da taron tattauna batun tattara kudaden shawo kan kalubalen sauyin yanayi a Paris

2023-06-23 17:03:40 CMG Hausa

A jiya Alhamis ne aka kaddamar da taron nazarin sabuwar yarjejeniyar samar da kudaden gudanar da ayyuka, masu nasaba da sauyin yanayi a birnin Paris na kasar Faransa, taron da ya hallara wakilai sama da 300 daga fannoni daban daban.

Cikin manyan jami’an da aka gayyata domin halartar taron, har da firaministan kasar Sin Li Qiang.

Cikin jawabin sa na bude taron, shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya ce tsarin tattara kudi na kasa da kasa riba ce ta manufofin baya, wanda hakan ta tabbatar da tasirin matakai da aka dauka. To sai dai kuma ba dukkanin matakan ne ke iya samar da nasarar da ake bukata a yanzu ba. Don haka wajibi ne a daidaita matakan na baya daidai da bukatun yanzu.

Kaza lika shugaba Macron, ya yi kira da a samar da karin kudade, na shawo kan kalubalen yaki da fatara, da kare mabanbantan halittu da sauyin yanayi.

Ana dai sa ran mahalarta taron na wannan karo, za su mayar da hankali ga tattauna muhimman batutuwa da suka shafi sauyin yanayi karkashin kananan taruka 6, da suka hada da na sauya fasalin tsarin tattara kudade na kasa da kasa, da dawo da kwarin gwiwar cimma nasarori, da gina kawancen tsara manufofi, da samar da kyakkyawan yanayin tafiya tare da sassa masu zaman kan su. (Saminu Alhassan)