logo

HAUSA

MDD ta ware dala miliyan 20 domin samar da tallafin abinci na gaggawa a arewa maso gabashin Najeriya

2023-06-21 10:36:42 CMG Hausa

 

MDD ta ware kudi har dalar Amurka miliyan 20, domin samar da tallafin abinci na gaggawa a jahohin Borno, da Adamawa da Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya.

Da yake tabbatar da hakan a jiya Talata, Farhan Haq, mataimakin kakakin babban magatakarda Antonio Guterres na MDD, ya ce za a samar da dala miliyan 9 ne daga assusun ayyukan gaggawa na majalissar, yayin da kuma ragowar dala miliyan 11, za su fito daga asusun agajin jin kai na Najeriya. Ya ce MDD za ta taimakawa gwamnatin Najeriyar wajen cimma nasarar samar da wannan tallafi.

Haq ya kara da cewa, tallafin zai kunshi kayan abinci, da dafaffen abinci ga mabukata, da tsaftacaccen ruwan sha, da ayyukan kiwon lafiya da tallafin noma. (Saminu Alhassan)