logo

HAUSA

Wakilin Sin ya bayyana matsayin kasarsa kan batun hakkin dan Adam yayin taron MDD

2023-06-21 11:02:16 CMG Hausa

Zaunannen wakilin kasar Sin dake ofishin MDD da sauran kungiyoyin kasa da kasa a birnin Geneva na kasar Switzerland Chen Xu, ya gabatar da manufofi da matsayin kasar Sin kan batun kare hakkin dan Adam, yayin taron hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD karo na 53 da ya gudana a jiya Talata, inda ya ce a halin yanzu, ana fuskantar babban kalubale a fannin kare hakkin dan Adam, don haka ya kamata a yi tunani sosai game da yadda za a raya harkokin kare hakkin dan Adam, da warware matsalar siyasantar da batun, bisa manufar girmama juna, da nuna adalci.

Chen Xu ya kara da cewa, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka wajen mai da aikin kula da al’ummomin kasar a matsayin aiki mafi muhimmanci, yayin da raya harkokin kare hakkin dan Adam ke gudana bisa hanya mafi dacewa da yanayin kasar.

A halin yanzu, kasar Sin na taka muhimmiyar rawa a fannin raya tattalin arziki a jihar Xinjiang, da yankin Tibet, da kuma a yankin Hong Kong na musamman, tare da kare yanayin zaman lafiya da lumana a wadannan wurare, da kuma raya harkokin kare hakkin dan Adam.

Bugu da kari, kasar Sin tana fatan yin hadin gwiwa da kasashen duniya, da ofishin jami’an MDD masu kula da harkokin hakkin dan Adam, domin raya aikin kare hakkin dan Adam a fadin duniya yadda ya kamata. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)