logo

HAUSA

Hukumar lafiya ta MDD ta kaddamar da aikin inganta lafiyar mata masu juna biyu a Somaliya

2023-06-19 11:01:16 CMG Hausa

A jiya Lahadi ne asusun kula da yawan jama'a na Majalisar Dinkin Duniya UNFPA ya bayyana cewa, ya hada kai da cibiyar ba da agajin jin kai ta Sarki Salman (KS relief) domin kaddamar da wani shiri na inganta lafiyar mata masu juna biyu da masu raino wadanda suka rasa matsuguninsu a Somaliya.  

Wakiliyar UNFPA a Somaliya Niyi Ojuolape ta ce shirin na nufin magance matsalolin kiwon lafiya masu mahimmanci na al'ummomi raukanannu, musamman mata da ’yan mata da ke fama da matsalar ƙaura da kuma matsalolin jin kai.

Shugaban KS-Relief na Somalia Yaziid Hamoud ya ce, aikin zai inganta samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya, da lafiyar mata, da kuma ingancin jama’a marasa galihu a yankuna shida.

Aikin zai haɓaka damar samun cikakkiyar kulawar gaggawa ta masu juna biyu da jarirai, da ƙarfafa iya ayyukan kiwon lafiyar haihuwa, da inganta tsarin samar da kayayyaki a Somaliya. (Yahaya)