logo

HAUSA

Ziyarar tawagar wanzar da zaman lafiya ta Afirka a Rasha da Ukraine ta ja hankali

2023-06-16 10:07:40 CMG Hausa

A yau ne, wata tawagar zaman lafiya da ta kunshi shugabanni daga kasashen Afirka ta Kudu, da Masar, da Comoros da sauran kasashen Afirka, za su isa Ukraine domin ziyarar, daga bisani kuma za ta ziyarci kasar Rasha. A baya shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramafosa ya bayyana cewa, mambobin tawagar za su saurari sharuddan kawo karshen rikicin da ke tsakanin Rasha da Ukraine, sannan kuma za su gabatar da shirye-shiryen samar da zaman lafiya a Afirka.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky, sun amince da karbar bakuncin tawagar shugabannin kasashen Afirka da za su gudanar da ayyukan samar da zaman lafiya a Moscow da Kiev.

A halin yanzu, ra'ayoyin jama'a a bangarori na rayuwa a Afirka na ganin cewa, ta’azzarar rikicin kasar Ukraine ya yi tasiri matuka ga nahiyar Afirka ta fannoni daban-daban, musamman a fannin tattalin arziki. Kasashen Rasha da Ukraine baki daya, su kasance kasashen dake kan gaba wajen fitar da abinci zuwa kasashen waje, kuma rikicin tsakanin Rasha da Ukraine shi ma ya kawo illa matuka wajen samar da abinci a Afirka. (Ibrahim Yaya)