logo

HAUSA

Wakilin Sin ya bukaci a kula da dangantakar kasa da kasa bisa doka

2023-06-16 14:54:48 CMG Hausa

Jiya Alhamis, aka gudanar da taron muhawara na babban taron MDD a hedkwatar MDD dake birnin New York, mai taken “kowa na da ikon amfani da doka: A gaggauta yin kwaskwarima domin gina zamantakewar al’umma mai zaman lafiya, da adalci, wadda ke tabbatar da moriyar kowa”. A nasa jawabin mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Dai Bing ya bayyana cewa, ya kamata a tsaya tsayin daka wajen tafiyar da harkokin dake shafar dangantaka a tsakanin kasa da kasa bisa doka.

Ya ce, tsari daya ne kawai a duniya, kuma shi ne tsarin kasa da kasa da ya ginu bisa dokokin kasa da kasa. Kasar Sin ba ta amince da wai “tsarin duniya bisa ka’idoji” da wasu kasashe suka tsara, suka kuma tilastawa gamayyar kasa da kasa don su bi wannan tsari, a maimakon bin dokar kasa da kasa. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)