logo

HAUSA

Tunisiya ta gano manyan damammaki wajen inganta huldar kasuwanci da zuba jari da kasar Sin

2023-06-16 11:24:36 CMG Hausa

Jami'an cinikayya da ’yan kasuwa na kasar Tunisiya, sun zayyana wasu manyan damammakin da ake da su na inganta huldar kasuwanci da zuba jari da kasar dake arewacin Afirka da kasar Sin.

Mataimakiyar shugaban farko ta gamayyar kungiyoyin ’yan kasuwa na kasar da ake kira (CONECT International) Salma Elloumi ce ta bayyana hakan, a yayin taron tattalin arziki da kasuwanci tsakanin Tunisiya da Sin, da ya gudana a Tunis, babban birnin kasar. Tana mai cewa, za a cimma nasarar hakan ne kuwa, duba irin damammakin da ake da su a fannonin fasahar zamani marasa gurbata muhalli, da makamashi da ake iya sabuntawa, da magunguna, da gine-gine da ababen more rayuwa, da kiwon lafiya, da yawon shakatawa da fasahar sadarwar zamani.

An shirya taron ne domin amfanin tawagar tattalin arziki na kamfanoni 20 na kasar Tunisia, wadanda za su ziyarci kasar Sin domin halartar bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka karo na 3 da za a gudanar a birnin Changsha dake yankin tsakiyar kasar Sin daga ranar 29 ga watan Yuni zuwa ranar 2 ga watan Yuli. (Ibrahim)