logo

HAUSA

Dai Bing ya yi kira ga kasa da kasa da su samar da yanayi na zaman lafiya

2023-06-15 10:01:57 CMG Hausa

Jiya Laraba, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Dai Bing ya gabatar da jawabi a taron muhawara game da al’adun zaman lafiya na babban taron MDD, inda ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su nuna fahimtar juna, da daukar matakan da suka dace wajen samar da yanayin zaman lafiya a duniya.

Ya ce, rashin fahimtar juna shi ne ya haddasa kalubaloli iri-iri da muke fuskanta a halin yanzu. Zurfafa fahimtar juna dake tsakaninmu yana bukatar girmama juna, da mu’amala cikin zaman lafiya, da hadin gwiwa don cimma moriyar juna, da kiyaye yanayin adalci na duniya, da aiwatar da ra’ayin cude-ni-in-cude-ka yadda ya kamata. Akwai kasashen dake neman raba dangantakar dake tsakanin kasa da kasa bisa hujjar dimokuradiyya, lamarin da ya bata fahimtar juna dake tsakanin kasa da kasa, da haddasa illa ga kasashen duniya.

Bugu da kari, ya ce, ya kamata a tsaya tsayin daka wajen shimfida zaman lafiya ta hanyar neman ci gaba, ajandar ci gaba mai dorewa ta MDD, da rahoton “ajandarmu” da babban magatakardan MDD ya fidda, za su kasance muhimman dabarun kawar da sabani, da shimfida zaman lafiya na dindindin. Ya kara da cewa, ya kamata gamayyar kasa da kasa su mai da hankali kan batun neman bunkasuwa, da yin hadin gwiwa domin samun ci gaba tare, da mai da hankali kan kalubalolin dake gaban kasashe masu tasowa, ta yadda al’ummomin kasa da kasa za su iya cin gajiyar sakamakon bunkasuwar duniya cikin yanayi na adalci. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)