logo

HAUSA

Za A Rika Inganta Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Honduras

2023-06-13 21:01:12 CMG Hausa

Da sanyin safiyar yau Talata 13 ga wata, kafofin yada labaru na kasar Honduras sun ruwaito a shafunansu cewa, an bude sabon babin raya hulda a tsakanin kasarsu da kasar Sin, tare da ambato lamba “17” sau da dama, wadda ma’anarta ita ce takardun fahimtar juna guda 17 da kasashen 2 suka daddale, a fannin hada kai a sassa daban daban.

Kasar ta Honduras, muhimmiyar kasa ce a yankin Tsakiyar Amurka, kuma sabuwar abokiyar kasar Sin ce. A ranar 26 ga watan Maris na bana, kasashen Sin da Honduras sun kafa huldar jakadanci a tsakaninsu bisa ka’idar “kasar Sin daya tak a duniya”. Honduras ta zama ta 182, a jerin kasashen da suka kulla huldar jakadanci da kasar Sin.

A Jiya Litinin ne shugaba Xi Jinping na kasar Sin, da takwararsa ta Honduras Iris Xiomara Castro Sarmiento, wadda ke ziyarar aiki a kasar Sin, suka yi shawarwari, inda shugaba Xi ya jinjina wa yadda Castro ta tsai da kuduri mai matukar muhimmanci a tarihi, da kuma nuna aniyar siyasa.

A lokacin ziyarar shugaba Castro a kasar Sin, Honduras ta gabatar da rokon shiga bankin New Development Bank, kuma kasashen 2 sun amince da kaddamar da shawarwari kan yarjejeniyar ciniki cikin ‘yanci, sun kuma daddale takardar fahimtar juna kan hadin gwiwar aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, tare da ba da sanarwar hadin gwiwar cimma ra’ayi daya.

Har ila yau, shugabannin kasashen 2 sun tsara shiri kan raya hulda a tsakanin kasashen 2, za kuma a kaddamar da hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki, da ciniki, da raya al’adu da dai sauransu, a kokarin samun ci gaba tare, ta yadda al’ummun kasashen 2 za su kara samun alherai. ‘Yan kasuwan Honduras suna da yakinin cewa, jatanlanle, da kankana, da kofi na Honduras, za su samu amincewa sosai a kasar Sin. Haka kuma, Honduras na maraba da kamfanonin Sin, da su zuba jari, da shiga ayyukan raya tattalin arzikin Honduras. (Tasallah Yuan)