logo

HAUSA

Ministan wajen Saudiyya ya yaba da habakar hadin gwiwar Sin da kasashen Larabawa

2023-06-12 12:34:19 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Saudiyya Faisal bin Farhan Al Saud ya bayyana a jiya Lahadi cewa, taron kasuwanci na kasashen Larabawa da Sin karo na 10, wata dama ce ta karfafa dangantakar abokantaka ta tarihi tsakanin kasashen Larabawa da kasar Sin, da gina makoma mai kyau da za ta amfani bangarorin biyu, da inganta zaman lafiya da ci gaba a duniya.

Ministan ya bayyana hakan ne a wajen bikin bude taron da aka fara a Riyadh, babban birnin kasar Saudiyya a ranar Lahadi.

Ministan na Saudiyya ya jaddada sadaukarwar da yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya, kuma firaministan kasar Mohammed bin Salman Al Saud ya yi na karfafa alaka mai dadadden tarihi da ci gaba tsakanin kasashen Larabawa da kasar Sin a dukkan fannonin zuba jari.

Ya kuma kara da cewa, taken taron "hadin gwiwa don samun wadata" ya nuna matukar muhimmanci, damammaki, daidaito da kuma hangen nesa daya da ke da nasaba da zuba jari da huldar kasuwanci tsakanin kasashen Larabawa da kasar Sin.

Kasar Sin ita ce babbar abokiyar cinikayyar kasashen Larabawa, kuma yawan mu'amalar cinikayya tsakanin sassan biyu ya kai dalar Amurka biliyan 430 a shekarar 2022, wanda ya karu da kashi 31 cikin 100 daga shekarar 2021, in ji ministan. (Yahaya)