logo

HAUSA

Kasashen BRICS na kokarin inganta aikin warware rikicin Ukraine

2023-06-12 13:31:27 CMG Hausa

Kwanan baya, manzon musamman dake kula harkokin kasar Afirka ta Kudu da nahiyar Asiya da kasashen BRICS, Anil Sooklal ya yi tsokaci kan rikicin Ukraine a yayin da yake zantawa da wakilin Babban Gidan Rediyo da Talabijin na Kasar Sin (CMG) dake kasarsa, inda ya ce, dukkanin kasashen BRICS, ciki har da kasar Afirka ta Kudu suna goyon bayan warware rikicin Ukraine ta hanyar yin shawarwari, domin kawo karshen rikicin baki daya.

Yana mai cewa, dukkanin kasashen BRICS suna kokarin neman hanya mai dacewa wajen warware rikicin, sun kuma tattauna batun a yayin taron ministocin harkokin wajen kasashen BRICS, da kuma sauran taruka. Lamarin da ya sake jaddada aniyar kasashen BRICS wajen warware rikicin Ukraine ta hanyar yin shawarwari da kuma kawo karshen rikicin.

Haka kuma, ya ce, shawarar tabbatar da zaman lafiya da shugabannin kasashen Afirka suka fitar, ta shafi kasashen Afirka guda shida. Kana, shugabannin wadannan kasashe, ciki har da shugaban kasar Afirka ta Kudu Matamela Cyril Ramaphosa za su kai ziyara kasashen Ukraine da Rasha domin kokarin aiwatar da aikin shiga tsakani wajen warware rikicin Ukraine ta hanyar diflomasiyya.

A watan Agusta na bana, za a kira taron kolin shugabannin kasashen BRICS na shekarar 2023 a kasar Afrika ta Kudu, dangane da wannan lamari, Anil Sooklal ya ce, a matsayin kasa mai masaukin baki ta karba-karba, kasar Afirka ta Kudu tana mai da matukar hankali kan wannan muhimmin taro, tana kuma shirya harkokin da abin ya shafa kamar yadda ake fatan. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)