logo

HAUSA

Shugabar kasar Honduras ta fara ziyara a kasar Sin

2023-06-09 15:27:30 CMG Hausa

Shugabar jamhuriyar Honduras Iris Xiomara Castro Sarmiento, ta isa birnin Shanghai da safiyar yau Juma’a, inda ta fara ziyarar da zai kai ta har zuwa ranar 14 ga watan Yuni, bisa gayyatar shugaban kasar Sin Xi Jinping. 

Wannan shi ne karo na farko da wani shugaban kasar Honduras ya kawo ziyara kasar Sin. Yayin ziyarar, shugabannin biyu za su yi wata ganawa mai muhimmanci domin tsara makomar ci gaban dangantakar kasashen Sin da Honduras. (Fa’iza Mustapha)