logo

HAUSA

Sin za ta yi aiki tare da tarayyar Turai wajen maido da musaya tsakanin al’ummunsu

2023-06-09 11:12:58 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce Sin a shirye take, da ta yi aiki tare da kungiyar tarayyar Turai ta EU, ta yadda za a kai ga dawo da musaya tsakanin al’ummun sassan biyu a dukkanin matakai, da kara ingiza cin gajiyar hadin gwiwa tsakanin su a dukkannin fannoni.

Wang Wenbin ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, lokacin da yake amsa tambayar da aka yi masa, game da rahotannin baya bayan nan dake cewa kuri’un jin ra’ayin jama’a kan alakar Turai da kasashen waje, sun tabbatar da ra’ayi mafi rinjaye na kasancewar Sin abokiyar tafiya ta hakika. Kuri’un sun kuma tabbatar da matsayin Sin da Turai na kasancewa abokan arziki, ba masu adawa da juna ba.

Wang ya kara da cewa, har kullum Sin a shirye take da ta yi aiki tare da kungiyar tarayyar Turai ta EU, wajen wanzar da fahimtar juna da shugabannin su suka amincewa, da nacewa bin turba ta-gari, da dorewa kan kyakkyawar huldar sassan biyu, da kara fadada dunkulewar manufofinsu na samun ci gaba tare, da yaukaka dangantakarsu a dukkanin fannoni, ta yadda za a kai ga karfafa, da fadada fannonin hadin gwiwa tsakanin Sin da EU, da samar da karin daidaito, da tabbaci, musamman a wannan lokaci da duniya ke fuskanta yanayi na wahala da rashin tabbas.  (Saminu Alhassan)