logo

HAUSA

Bankin duniya ya daga hasashensa na ci gaban tattalin arzikin duniya da na kasar Sin a bana

2023-06-07 16:21:24 CMG Hausa

Bankin duniya ya fitar da sabon rahoton hasashen tattalin arzikin duniya a ranar 6 ga watan Yuni, inda ya yi hasashen cewa, tattalin arzikin duniya zai bunkasa da kashi 2.1% a shekarar 2023, wanda ya karu da kashi 0.4% bisa kiyasin da aka yi a watan Janairu, amma duk da haka bai kai na  shekarar 2022 wanda ya kai kashi 3.1% ba. Tattalin arzikin kasar Sin kuma zai bunkasa ya karu da kashi 5.6 cikin 100 a shekarar 2023, wanda ya karu da kashi 1.3% bisa hasashen bankin a Janairu.

Rahoton ya yi nuni da cewa har yanzu tattalin arzikin duniya yana cikin wani yanayi maras tabbas a dalilin tasirin annobar COVID-19, rikicin Rasha da Ukraine, da kuma tsauraran manufofin kudi.  Hauhawar kudin ruwa a Amurka cikin sauri yana haifar da manyan ƙalubale ga kasuwanni masu tasowa da ƙasashe masu ci gaba, wanda ke haifar da yuwuwar matsalar hada-hadar kuɗi.(Yahaya)