logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi kira da mayar da batun ci gaba tsakiyar ajandar kasa da kasa

2023-06-07 13:41:38 CMG Hausa

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a majalisar dinkin duniya Dai Bing, ya yi jawabi a gun taron shekara shekara na 2023 da aka yi tsakanin ofisoshin gudanarwar na shirin raya kasa na majalisar dinkin duniya (UNDP), da asusun kula da yawan jama'a na majalisar dinkin duniya (UNFPA) da ofishin kula da ayyuka na majalisar dinkin duniya (UNOPS) a ranar 6 ga Yuni, inda ya yi kira da a mayar da batun ci gaba a tsakiyar ajandar kasa da kasa.

Dai Bing ya ce, ajandar ci gaba mai dorewa ta 2030 ta wuce rabin lokacinta, kuma ci gaban aiwatar da ita na tafiyar hawainiya. Kasar Sin tana son gabatar da wasu shawarwari kamar haka: na farko, samar da yanayi mai kyau wajen tabbatar da ci gaba. Na biyu, mutunta ikon mallaka da jagorancin kasashen da ke cikin shirye-shiryen. Na uku, tara albarkatu da yawa don ci gaba. Na hudu, mu ƙarfafa haɗin gwiwa. (Yahaya)