logo

HAUSA

Shugabar Honduras za ta ziyarci kasar Sin

2023-06-07 16:09:17 CMG Hausa

Bisa gayyatar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi mata, shugabar kasar Honduras Iris Xiomara Castro Sarmiento, za ta ziyarci kasar Sin tsakanin ranaikun 9 zuwa 14 ga watan Yunin nan, kamar dai yadda kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta sanar da hakan a Larabar nan. (Saminu Alhassan)