logo

HAUSA

Sin: Yin Katsa-landan Da Sanya Takunkumin Kashin Kai Ba Za Su Warware Batun Tsakiyar Afirka Ba

2023-06-06 10:33:39 CMG Hausa

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Dai Bing, ya jaddada jiya Litinin cewa, yin katsa-landan da sanya takunkumin kashin kai, ba za su warware batun tsakiyar Afirka ba.

A yayin muhawarar da kwamitin sulhu ya shirya kan batun tsakiyar Afirka, Dai Bing ya ce, abubuwan da suka faru a wasu kasashen Afirka sun nuna cewa, wajibi ne a dogara da karfin kasashen nahiyar wajen daidaita batun Afirka. Kana wajibi ne kasashen duniya su mutunta ikon mulkin kan kasashen Afirka, da ikonsu na daidaita batun, a kokarin samar da kyakkyawan karsashi na kiyaye kwanciyar hankali ta fuskar siyasa a yankin.

Ya ce kasar Sin na da imanin cewa, ya kamata kasashen duniya su gudanar da bincike kan ayyukan kiyaye hakkin dan Adam bisa sanin ya kamata, da hakikanin halin da kasashe masu ruwa da tsaki suke ciki, da kuma bukatun jama’arsu, su kuma kauce wa kiyaye hakkin dan Adam a fatar baka kawai, kuma kar su yi amfani da batun kare hakkin dan Adam domin tsoma baki cikin harkokin cikin gidan wasu kasashe.

Jakadan na kasar Sin ya kara da cewa, yadda wasu muhimman rukunonin tattalin arziki suka aiwatar da manufofin hada-hadar kudi da ba su dace ba, da tura barazanar tattalin arziki da matsalolin kudi da suke fama da su kan wasu kasashe, da satar dukiyoyin kasashe masu tasowa, barazana ce mafi muni ga kasashen Afirka masu tasowa. Don haka dole ne kasashe masu sukuni, da hukumomin kudi na kasa da kasa, su fahimci matsalolin da kasashen da ke yankin suke fama da su, su cika alkawarin bayar da tallafin raya kasa, da kiyaye zuba kudaden jin kai, a kokarin taimakawa wadannan kasashe jure wahalhalu. (Tasallah Yuan)