logo

HAUSA

Sin ta gabatar da kakkarfan korafi ga IAEA game da shirin Japan na zubar da gurbataccen ruwan tashar nukiliyar Fukushima cikin teku

2023-06-06 16:31:50 CMG Hausa

A jiya Litinin ne daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya na kasar Sin, kuma daraktan kasar Sin a hukumar gudanarwar IAEA Zhang Kejian, ya halarci taron IAEA na watan Yunin nan a birnin Vienna tare da gabatar da jawabi.

Cikin jawabin nasa, Zhang Kejian ya soki lamirin kasar Japan, na shirin zubar da dagwalon nukiliyar Fukushima cikin teku. Zhang Kejian ya ce batun shigar da wannan gurbataccen ruwa cikin teku, muhimmin lamari ne da ya shafi harkokin muhallin tekunan duniya, da fannin kiwon lafiyar daukacin al’ummun kasa da kasa, ba wai batu ne da ya shafi kasar Japan kadai ba.

Don haka jami’in ya yi kira ga gwamnatin Japan, da ya mayar da hankali ga damuwar kasashen duniya, ta kuma sauke nauyin dake wuyanta na kare hakkokin al’ummar duniya. Zhang Kejian ya ce ya kamata Japan din ta bi hanyoyi na kimiyya, a fayyace kuma marasa hadari, wajen kawar da dagwalon na Fukushima, tare da amincewa da sanya idon sassan kasa da kasa. (Saminu Alhassan)