logo

HAUSA

Yadda Amurka ke tunkarar abubuwa ta fuska biyu ba abu ne mai yiwuwa ga Sin ba

2023-06-05 21:45:38 CMG Hausa

A kwanakin baya, kasar Amurka ta sake bayyana cewa, tana da sabani sosai a alakarta da kasar Sin, a bangare guda kuma, sakataren tsaron kasar Amurka Austin ya takali kasar Sin a yayin taron tattaunawa na Shangri-La karo na 20, inda ya ambaci batun tekun Taiwan da abin da ake kira, wai ‘yancin yin zirga-zirga. A sa’i daya kuma, jiragen ruwan yaki na Amurka sun nemi ratsa mashigin tekun Taiwan, amma kuma sun yi ikirarin cewa, bangaren kasar Sin ya “tunkare su”. A daya hannun kuma, mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka mai kula da harkokin waje na gabashin Asiya da tekun Pasifik Conda, ya ziyarci kasar Sin a ranar 4 ga wata, don neman tattaunawa da kasar Sin.

Mutane ba su saba da tsarin yau da kullum na shiga cikin rikici yayin yin tattaunawa da hadin gwiwa ba. A alakarta da kasar Sin, sabanin yanayin da Amurka ke ciki a hakika shi ne dabarunta na ketare. Wasu manazarta na ganin cewa, kasa mai karfi kamar Amurka, wadda ta saba da mamaye kasashen duniya, ba ta da ma’anar diflomasiyya a tsarinta. (Ibrahim)