logo

HAUSA

Me ya sa BRICS ke kara samun karbuwa daga kasashen duniya

2023-06-04 22:19:09 CMG Hausa

“Kasashen BRICS na kasance tamkar maganadiso, wanda ke ta jawo masu neman tabbatar da zaman lafiya da hadin gwiwa……Mu ma Venezuala, muna fatan zama daya daga cikin kasashe mambobin BRICS.” Shugaban kasar ta Venezuala Nicolás Maduro Moros ne ya fadi haka a kwanan baya a gun taron manema labarai da aka shirya bayan ganawarsa da takwaransa na kasar Brazil.

Daga ranar 1 zuwa 2 ga wata, an gudanar da taron ministocin wajen kasashen BRICS a birnin Cape Town na kasar Afirka ta kudu, kuma fadada mambobin kungiyar na daya daga cikin muhimman batutuwan da aka tattauna a gun taron. Bayanai na cewa, kasashe da dama ciki har da kasashen Afirka irinsu Aljeriya da Masar, duk sun bayyana burinsu na zama mambobin kungiyar BRICS, kafin wannan kuma, wakilin musamman na gwamnatin kasar Afirka ta kudu mai kula da harkokin Asiya da gabas ta tsakiya da kuma kasashen BRICS, Anil Sooklal ya bayyana cewa, “Kusan muna samun sakwannin neman zama mambar BRICS a kowace rana.”

Amma me ya sa BRICS ke kara farin jini?

In mun yi nazari, za mu gano cewa, hakan ya faru ne sabo da na farko, kungiyar BRICS na jawo hankalinsu ne sabo da yadda take neman hadin gwiwa da ci gaba, a maimakon rarrabuwar kawuna da yin fito na fito da juna. Ba kamar yadda Amurka da kawayenta na yammacin duniya su kan kulla kawance ne don su tinkari wani, tsarin BRICS tun farkon kafuwarsa yana mai da hankali ne a kan inganta hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa. A sa’i daya kuma, ba ya da niyyar yin fito na fito da kasashen yamma ko kuma maye gurbinsu.

Na biyu kuma, kasashen BRICS na dukufa a kan daidaita tsarin gudanar da harkokin duniya da ma kiyaye moriyar kasashe masu tasowa, sakamakon yadda kasashe masu tasowa ke fuskantar karancin wakilci da ma jin muryarsu a harkokin duniya. Tun kafa shi, tsarin na BRICS ya yi ta kokarin fito da muryar kasashe masu tasowa a duniya da kuma kare moriyarsu ta bai daya. In mun dauki misali da asusun ba da lamuni na duniya(IMF), wanda kasancewarsa muhimmiyar hukumar kula da hada-hadar kudi ta duniya, amma kuma ta dade tana wakiltar kasashen yamma ne kawai. Sai dai bisa kwaskwarima da aka sha yiwa asusun, tsarin BRICS ya kyautata wakilcin kasashe da tattalin arzikinsu ke saurin bunkasa a hukumar ta IMF. A gun taron ministocin wajen BRICS da aka gudanar a wannan karo kuma, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Ma Zhaoxu ma ya sake jaddada cewa, ya kamata a kara wakilcin kasashe masu tasowa tare da kara jin muryarsu a harkokin duniya.

Na uku, BRICS na mai da hankali ne a kan cimma hakikanan nasarori da za su amfanawa kasashe masu tasowa. In mun dauki misali da bankin NDB da kasashen BRICS suka kafa, wanda ya kasance banki na tsakanin kasa da kasa na farko da kasashe masu tasowa suka kafa, wanda tun kafuwarsa a shekaru 7 da suka wuce har zuwa yanzu, rancen kudin da ya samar har ya kai dala biliyan 32, wanda aka zuba su a fannonin bunkasa ababen more rayuwa da ma wasu ayyuka na tabbatar da dauwamammen ci gaba a kasashen BRICS. Musamman ma a lokacin da aka fuskanci annobar Covid-19, Bankin ya samar da kudin agajin gaggawa na dala biliyan 10 ga kasashe mambobin BRICS.

Yadda karin kasashe ke neman zama mambobin BRICS ya shaida mana bukatu na bai daya na kasashe masu tasowa, wato yin hadin gwiwa da juna don tabbatar da bunkasuwar juna, da kara tabbatar da adalcin tsarin duniya.(Lubabatu Lei)