logo

HAUSA

Sama da mutane 200 sun rasu sakamakon hadarin jirgin kasa a Indiya

2023-06-03 15:59:19 CMG Hausa

 

Rahotanni daga kasar Indiya na cewa, sama da mutane 200 sun rasu, baya ga wasu 900 da suka jikkata, yayin wani mummunan hadarin jirgin kasa da ya rutsa da wasu jirage 3 da yammacin jiya Juma’a, a jihar Odisha ta gabashin kasar.

Cikin wani sakon Tiwita da ya wallafa a shafin sa, babban sakataren gwamnatin jihar ta Odisha Pradeep Jena, ya ce a kalla mutane 207 ne suka rasa rayukan su, kana wasu kimanin 900 suka jikkata, kuma mai yiwuwa adadin mamatan ya karu. Ya ce hadarin ya auku ne da misalin karfe 7:20 na dare bisa agogon wurin, a kusa da tashar Bahanaga Bazar ta gundumar Balasore, kimanin kilomita 171 daga garin Bhubaneswar, na arewa maso gabashin jihar ta Odisha.

Mahukuntan jihar dai sun ce jirgin Coromandel Express, mai bin layin Kolkata zuwa Chennai, ya yi taho mu gama da wani jirgin mai bin layin Yashwantpur zuwa Howrah, kuma bayan ya goce daga layin da yake kai sai ya fada wani layin na daban. Hadarin ya kuma shafi wani jirgin na dakon kaya.    (Saminu Alhassan)