logo

HAUSA

Kwamitin sulhu ya goyi bayan kasancewar MDD a Sudan

2023-06-02 09:20:19 CMG Hausa

Shugabar kwamitin sulhun MDD ta wannan karo Lana Zaki Nusseibeh ta bayyana cewa, kwamitin sulhun majalisar yana goyon bayan ci gaba da kasancewar MDD a kasar Sudan, ana kuma sa ran kwamitin zai sabunta wa’adin aikin majalisar a kasar.

Zaunanniyar wakiliyar hadaddiyar daular Larabawa (UAE) a MDDr wadda kasarta ke rike da shugabancin karba-karba na kwamitin sulhu na watan Yuni, ta bayyana a tattaunawar sirri da aka yi ranar Laraba kan halin da ake ciki a Sudan cewa, mambobin kwamitin sulhun majalisar sun goyi bayan ci gaba da kasancewar aikin majalisar a kasar Sudan.

Lana ta shaidawa taron manema labarai kan zaben kasarta a matsayin wadda za ta shugabancin kwamitin sulhun cewa, sakamakon taron wani kwakkwaran alkawari ne daga mambobin majalisar game da irin muhimmmin aikin dake gaban majalisar kan rikicin kasar, tana mai cewa, hakan ya fayyace komai a fili.

A game da taron kuwa, jami’ar ta bayyana cewa, tawagar UNITAMS dake Sudan ta samu dukkan goyon bayan da ya dace, da ma goyon bayan kasancewar MDDr a Sudan, don taimakawa halin da ake ciki a makwabciyarta, har ma da yanayin da ake ciki a Sudan din.(Ibrahim)