logo

HAUSA

Majalisar dokokin Amurka ta amince da kudurin dokar kara yawan bashin da kasar za ta iya karba a karo na 103 tun shekarar 1945

2023-06-02 19:51:21 CMG Hausa

 

Bayan watanni ana takkadama tsakanin ‘yan jam’iyyun kasar, majalisar dokokin ksaar Amurka ta amince da kara yawan bashin da kasar za ta iya karba, bayan amincewar majalisar dattijan kasar a jiya Alhamis.

Wannan shi ne karo na 103 da aka kara yawan bashin da kasar za ta iya karba tun bayan shekarar 1945, haka kuma matakin ya ba kasar damar kaucewa shiga matsalar kudi.

Matakin yawan bashin ya kasance iyakar kudin da doka ta sahalewa gwamnati ta karba a matsayin rance domin samar da kudin gudanar da harkokinta.

Amurka ta kai iyakar yawan bashi na dala triliyan 31.4 ne a watan Janairu, adadin da ya kai  sama da kaso 120 na yawan GDPnta a shekara guda. An shafe watanni fadar White House da majalisar dokokin kasar suna ja-in-ja game da ka’idojin kara matakin yawan bashin, inda baitumalin kasar ta rika daukar tsauraran matakai domin kaucewa matsalar kudi.

Bayan sahalewar majalisar, za a tura kudurin ga ofishin shugaba Joe Biden domin ya rattaba hannu kafin kudurin ya zama doka. (Fa’iza)