logo

HAUSA

Ya Dace ‘Yan Siyasan Amurka Su Yi Tunani Kan Kalaman Elon Musk

2023-05-31 21:53:09 CMG Hausa

Bayan shekaru 3, shugaban kamfanin Tesla, Elon Musk ya sake ziyartar kasar Sin. Jiya Talata ne ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang ya gana da shi a birnin Beijing, inda Musk ya ce, muradun Sin da na Amurka na hade da juna. Kuma Tesla na adawa da katse tsarin samar da kayayyaki da rarrabuwar bangarori.

Yayin da huldar da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka ke fuskantar matsaloli, Musk ya bayyana ra’ayoyin wasu ‘yan kasuwar Amurka, wadanda kamata ya yi gwamnatin Amurka ta saurara a tsanake.

Tun daga farkon shekarar bana, manyan jami’an shahararrun kamfanonin Amurka ciki had da Musk sun ziyarci kasar Sin daya bayan daya, yayin da gwamnatinsu ta Amurka take ta ikirarin katse tsarin samar da kayayyaki da rarrabuwar bangarori, lamarin da ya nuna cewa, bunkasuwar kasar Sin, kyakkyawar dama ce ta kasa da kasa.

‘Yan kasuwa za su zuba jari a duk inda za su samu riba, ko ba haka ba? Hadaddiyar kungiyar ‘yan kasuwar Amurka ta kasar Sin ta gabatar da sakamakon bincike dake cewa, kamfanonin Amurka da ke nan kasar Sin da yawansu ya kai 66% sun shirya kiyayewa ko kara zuba jari a kasar Sin a cikin shekaru 2 masu zuwa. Haka kuma, kamfanonin Amurka suna da yakini kan kasuwar kasar Sin, lamarin da ya nuna cewa, kamfanonin Amurka sun fahimci abun da gwamnatin Amurka take yi na dakile ci gaban kasar Sin, zai illata moriyarsu. Kuma ba su son lalata moriyarsu sakamakon harkokin siyasa.

Sanin kowa ne cewa, Sin da Amurka na hade da juna ta fuskar tattalin arziki. Hadin gwiwa a tsakaninsu domin samun moriyar juna ya dace da muradunsu da ma muradun kasashen duniya. Abubuwan da suka faru sun sha tabbatar da lamarin. Kasar Sin har kullum tana nuna sahihanci kan kyautata hulda a tsakaninta da Amurka. Amma ana bukatar Amurka ita ma ta dauki matakai.(Tasallah Yuan)