logo

HAUSA

Sin na fatan bangaren Amurka zai yi hadin gwiwa da sabon jakadan Sin dake kasar

2023-05-24 21:35:18 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce tana fatan bangaren Amurka zai samar da goyon baya da kyakkyawan yanayin aiki ga sabon jakadan Sin a Amurka Xie Feng, ta yadda zai kai ga cimma nasarar aikin da ya sanya gaba, bayan isar sa birnin Washington a jiya Talata.

Da take bayyana wannan matsaya ta ma’aikatar wajen kasar Sin a yau Laraba, kakakin ma’aikatar Mao Ning, ta ce jakadan muhimmin jami’i ne dake zama gadar tattaunawa, da hadin gwiwa tsakanin Sin da Amurka. Kaza lika a cewar ta, alakar Sin da Amurka na da matukar muhimmanci ga kasashen biyu, da ma duniya baki daya. Mao Ning ta kuma yi kira ga bangaren Amurka, da ya hadu a tsakiya da tsagin kasar Sin, wajen cimma moriyar sassan biyu da al’ummun su. Tana mai cewa, kamata ya yi kasashen biyu su karfafa tattaunawa don shawo kan banbance banbancen su, da ingiza hadin gwiwar su, kana su hanzarta maido da huldar dake tsakanin su kan turba ta gari, mai inganci da wanzuwar ci gaba. (Saminu Alhassan)