logo

HAUSA

Sin da kasashen nahiyar Afirka na kara amincewa da juna

2023-05-18 16:22:35 CMG HAUSA

DAGA Saminu Hassan

A baya bayan nan masharhanta na ci gaba da fashin baki kan yadda alakar kasar Sin da sauran kawayenta na Afirka ke kara yaukaka ta fannoni daban daban. Ana kuma iya ganin shaidar hakan, idan aka dubi yadda manyan jami’an sassan biyu ke ta ziyartar juna, da tattaunawa, da kara jaddada burin kasashensu na karfafa cudanya da yin tafiya tare.

Ko da a cikin makon nan ma yayin da shugaban zaunannen kwamitin majalissar wakilan jama’ar kasar Sin Zhao Leji ke ziyarar aiki a kasar Senegal, ya jaddada manufar kasar Sin ta ci gaba da goyon bayan kasashen nahiyar Afirka, a fannin wanzar da zaman lafiya da samar da ci gaba.

Ko shakka babu, kasar Sin na nacewa matakan bunkasa alakarta da sauran kasashe masu tasowa, kamar yadda hakan ke gudana a zahiri, inda hadin gwiwar sassan a dukkanin matakai ke kara bunkasa yadda ya kamata.

A nasu bangare kuwa, kasashen Afirka na ta kara rungumar manufofin cimma moriyar juna tare da kasar Sin, karkashin shawarwari da manufofin da suka amincewa tare da kasar ta Sin. Karkashin hakan, kasashen Afirka da dama sun ci gajiya daga shawarar “ziri daya da hanya daya”, da manufofin samar da ci gaba da ake gudanarwa karkashin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC da dai sauran su.

Don haka ne ma masu fashin baki ke ganin shaidun gani da ido sun riga sun tabbatar da aniyar Sin, na ci gaba da fadada hadin gwiwa da kasashen Afirka, da zurfafa musaya a fannonin raya al’adu, da ilimi, da kiwon lafiya. Yayin da su kuma a nasu bangare, kasashen nahiyar ta Afirka ke fatan dorewar wannan kyakkyawar dangantaka, wadda ke haifar da tarin moriya ga al’ummun su. (Saminu Hassan)