logo

HAUSA

Wane kuzari ne ke karfafawa Sin da kasashen tsakiyar Asiya “su tsira tare su gudu tare”?

2023-05-17 14:25:49 CMG Hausa

Daga gobe Alhamis zuwa jibi Juma’a ne za a gudanar da taron kolin Sin da kasashen tsakiyar Asiya karo na farko, a birnin Xi’an, fadar lardin Shaanxi dake arewa maso yammacin kasar Sin. Tun bayan da Sin ta kulla abokantakar diplomassiya tare da kasashen tsakiyar Asiya a shekarar 1992, dangantakar dake tsakaninsu ta fuskanci kalubalolin da sauyin yanayin kasa da kasa ya haifar. Ko da yake dangantakar tasu ta samu babban ci gaba, inda ta ingantu daga dangantakar makwabta zuwa dangantaka bisa manyan tsare-tsare, da kuma abokantaka bisa manyan tsare-tsare, yayin da hadin gwiwarsu a fannoni daban daban ya samu ci gaba cikin sauri. To amma ko wane irin kuzari ne ya haifar da hakan?

Da farko dai bisa jagorancin shugabannin wadannan kasashe 6 suka bayyana a lokacin da suka kai wa juna ziyara. A cikin shekaru 10 da suka gabata, shugaban Sin Xi Jinping ya ziyarci kasashen dake tsakiyar Asiya har sau bakwai, kana ya yi rangadi a wasu muhimman garuruwan dake kan tsohuwar “hanyar siliki”, kamar Bukhara da Samarkand. A nasu bangare kuwa, shugabannin kasashen dake tsakiyar Asiya, su ma sun taba ziyartar wurare da dama a kasar Sin, kamar biranen Beijing da Shanghai da Qingdao.

Kasashen dake tsakiyar Asiya suna cikin tsakiyar nahiyar, kuma tattalin arzikinsu da na Sin, sun yi matukar dacewa da juna, musamman a shekarar 2013, a yayin ziyarar da shugaba Xi Jinping ya gudanar a kasar Kazakhstan, ya gabatar da shawarar “zirin tattalin arziki na hanyar silki” karo na farko, wadda ta samar da manyan damammakin ci gaban juna.

Sin da kasashe biyar na tsakiyar Asiya, kasashe ne masu tasowa, kuma dukkansu sun tsaya tsayin daka kan ra’ayin cudanyar bangarori daban daban, da kuma bin ka’idojin kasa da kasa, suna nuna goyon baya ga juna game da kare cikakken ikon mallakar kasa, da cikakken yankuna, da sauran manyan moriyarsu.

A halin yanzu, Sin da kasashen tsakiyar Asiya suna cikin matakin samun ci gaba mai muhimmanci. A sa’i daya kuma, kasashe daban daban suna fuskantar matsalar da canjin yanayin kasa da kasa ke haifarwa, inda mahalartansa ke karfafa fatansu na kawar da kalubaloli tare. 

A halin da ake ciki yanzu, taron kolin Sin da kasashen tsakiyar Asiya karo na farko ya zo kan gaba, inda ake sa ran zai baiwa bangarorin biyu damar inganta amincewa da juna bisa tsare-tsarensu, da kuma habaka hadin gwiwarsu a fannoni daban daban.  (Safiyah Ma)