logo

HAUSA

Yawan karin Amurkawa ‘yan asalin Afrika da suka mutu bisa hasashe a cikin shekaru 20 da suka gabata ya wuce miliyan 1.6

2023-05-17 21:01:01 CMG HAUSA

 

Kafar watsa labarai ta ABC dake Amurka, ta bayyana a yau Laraba cewa, mujallar kungiyar likitocin Amurka ta ba da rahoton cewa, daga shekarar 1999 zuwa 2020, yawan karin Amurkawa ‘yan asalin Afrika da suka mutu a kasar ya kai kimanin miliyan 1.63 bisa adadin da aka yi hasashe, daga cikinsu akwai maza dubu 997, da mata dubu 628. Bisa nazarin da aka yi kan lamarin, karin yawan mutanen da suka mutu shi ne adadin da ya wuce kiyasin da aka yi a baya.

Nazarin ya nuna cewa, ana ci gaba da fuskantar wannan matsala, kuma barkewar cutar COVID-19 ya tsananta gibin dake tsakanin sassan al’ummun da lamarin ke shafa. (Amina Xu)