logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Yi Kira Da A Taimaka Wa Kasashen Da Ke Yankin Sahel

2023-05-17 13:58:41 CMG Hausa

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Dai Bing, ya yi kira ga kasashen duniya da su kara bai wa kasashen dake yankin Sahel taimako, da goyon baya, daidai da bukatun da suke da su.

Dai Bing ya bayyana hakan ne a jiya Talata, yayin wani taron kwamitin sulhu, dangane da batun yankin na Sahel. Ya ce hadin kan kasashen da ke yankin Sahel, hanya ce da wajibi ne su bi, wajen daidaita kalubale tare. Kana yaki da ta’addanci, aikin gaggawa ne a halin yanzu. Kuma zurfafa bunkasuwa mai dorewa, babbar manufa ce ta daidaita matsala daga tushe.

Ya ce kamata ya yi kasashen duniya su gaggauta goyon bayan bunkasar yankin Sahel, su daga ajandar aikin ci gaban yankin zuwa muhimmin matsayi.

Dai Bing ya kara da cewa, kasar Sin na son hada kai da kasashen duniya, wajen kara ba da tallafi a fannonin yaki da talauci, da samar da isasshen abinci, da aikin gona da na kiwo, da samar da ababen more rayuwar jama’a, da tattara kudi domin ayyukan ci gaba. Ya ce a nata bangare, Sin na sa ran ganin hukumomin MDD, masu ruwa da tsaki sun kara taka rawar gani, wajen tattara albarkatu domin samun ci gaba. (Tasallah Yuan)