logo

HAUSA

Jakadan kasar Sin ya yi kira da a gaggauta shawo kan rikicin Ukraine

2023-05-16 14:30:35 CMG Hausa

Zaunannen jakadan kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya yi kira da a gaggauta shawo kan rikicin Ukraine ta hanyar samar da mafita a siyasance.

Zhang Jun ya kara da cewa, har yanzu rikicin na ci gaba da gudana, lamarin da ya jefa ana yin jin kai cikin matsanancin hali, baya ga mummunan tasirin rikicin dake ci gaba da bazuwa.

A cewarsa, ya kamata kasa da kasa su dauki matakan da suka dace na magance matsalolin jin kai da rikicin ya haifar tare da hada hannu wajen rage yanayin da ma tabbatar da dakatar da bude wuta tun da wuri.

Ya kara da cewa, a ko da yaushe, kasar Sin ta kasance mai goyon bayan zaman lafiya, kuma duk abun da take yi, na da nufin ingiza tattaunawar zaman lafiya. Ya ce Li Hui, wakilin musammam na kasar Sin kan harkokin Turai da Asia, ya fara ziyara a kasashen Ukraine da Poland da Faransa da Jamus da Rasha, a wani yunkuri na tuntubar bangarori daban daban game da batun shawo kan rikicin ta hanyar siyasa.

Bugu da kari, ya ce Sin ta shirya hada hannu da sauran kasashen duniya wajen ci gaba da kokari ba tare da gajiyawa ba, domin kawo karshen rikicin a siyasance.(Fa’iza Mustapha)