Taimkon Juna Tushen Dangantakar Sin Da Afrika
2023-05-16 19:08:04 CMG HAUSA
DAGA Faeza Mustapha
A farkon wannan mako ne shugaban kasar Eritrea Isaias Afwerki ya fara ziyarar aiki a kasar Sin, inda da yammacin jiya agogon Beijing, ya gana da shugaban kasar Sin Xi Jinping.
A ranar 24 ga wannan wata ne za a cika shekaru 30 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Eritrea, wanda ke tabbatar da irin dadaddiyar huldar dake tsakaninsu.
Da yake jawabi yayin ganawarsa da takwaransa na Eritrea, shugaban kasar Sin ya ce, ba tare da la’akari da yadda yanayin duniya zai kasance a nan gaba ba, mutunta juna da goyon baya da taimako, su ne za su kasance tubalin abota tsakanin Sin da Kasashen Afrika.
Idan ana batun mutunta juna, to ba shakka kasar Sin ta kasance mai mutunta ikon mulki da cikakken ’yancin kasashen Afrika, domin ta kasance kasar da ta samu ci gaba ba tare da bautar da su ko ci da guminsu ba, haka kuma ba ta yi musu katsalandan cikin harkokinsu na gida. A ko da yaushe, kasar Sin ta kan nuna girmamawa da kwarin gwiwarta kan karfin kasashen Afrika, inda take bayyana cewa, al’ummar Afrika su suka san matsalolinsu, kuma su ne za su iya samar da mafita, wannan hali ne na dattako da sanin ya kamata. Har ila yau, ita ce mai karfafa musu gwiwar lalubo hanyoyin da suka dace da su na samun ci gaba, ba tare da arowa daga waje ba. Wannan ya nuna matsayinta na babbar kasa da kuma burinta na ganin sun tsaya da kafafunsu, sun samu ci gaba ba tare da dogaro da wasu bangarori da za su gindaya musu sharuda ko danne su ko kuma yi musu katsalandan ba. Su ma a nasu bangare, mutuncin suke nunawa ta yadda suke amincewa da manufar kasancewar Sin daya tak a duniya, da goyon bayan matakan tabbatar da tsaro da take dauka a cikin gida da kuma kauracewa tsoma baki cikin harkokinta na cikin gida.
Taimako kuwa, ba zai misaltu ko ya kirgu ba. Ko a wannan lokaci da duniya ke fuskantar rashin tabbas da halin son kai daga manyan kasashe, kasar Sin ta tsaya kan bakanta na taimakawa kasashen Afrika. Kama daga ababen more rayuwa, fasahohin ayyukan gona da kiwon lafiya da tsaro da cinikayya da sauransu. Kasar Sin tana bude kofarta ga kasashen Afrika domin su shigo su ci gajiyar babbar kasuwarta, haka kuma tana karfafawa kamfanoninta da masu zuba jari gwiwar shiga kasashen Afrika domin su zuba jari. A nasu bangare, kasashen Afrika sun kasance masu maraba da kayayyaki kirar kasar Sin da bude kofa ga kamfanonin da ’yan kasuwa Sinawa a kasashensu.
Nasarori da kyakkyawan tasirin dangantakar bangarorin biyu a bayyane yake, domin Sin da Afrika sun zarce abokai, sun koma ’yan uwa, su kasance masu martaba juna da cin moriyar juna da kuma neman ci gaba na bai daya, ba tare da son ganin faduwar daya daga cikinsu ba. (Faeza Mustapha)