logo

HAUSA

Amurka ba za ta cimma yunkurin taron dangi bisa fakewa da batun Taiwan ba

2023-05-14 16:11:41 CMG Hausa

Kwanan baya sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken, ya fitar da wata sanarwa, inda ya bukaci hukumar kiwon lafiya ta duniya da ta gayyaci wakilin yankin Taiwan, ya halarci babban taron hukumar a bana, a matsayin ‘dan kallo. Wannan wani sabon mataki ne da Amurka ta dauka kan batun Taiwan, wanda wasu kafofin watsa labaran kasa da kasa ke ganin cewa, wata kila za a sake baza ra’ayin wai kasar Sin tana jawo kalubale ga duniya, a gun taron kolin G7 da za a kira. Haka kuma an yi hasashen cewa, za a kara mai da hankali kan batun Taiwan yayin taron.

A cikin ‘yan shekarun da suka gabata, wasu kasashen yamma, musamman ma Amurka sun baza jita-jita kan batun Taiwan, amma a bayyane yake cewa, matakan da masu neman ‘yancin Taiwan suka dauka da goyon bayan da wasu rukunonin siyasa na kasa da kasa ke ba su, sun kasance kalubale mafi tsanani ga zaman lafiya a zirin Taiwan, kuma su ne suke tsananta yanayin da zirin ke ciki.

Batun Taiwan ya shafi babbar moriyar kasar Sin. Kasashen duniya sun riga sun cimma matsaya guda kan manufar “kasar Sin daya tak a duniya”, kuma manufar ta kasance ka’ida kuma tushe, yayin da ake tafiyar da huldar kasa da kasa, haka kuma ita ce tushen siyasar kasar Sin yayin da ta ke kulla huldar diplomasiyya da sauran kasashen duniya.

Hakika wasu kasashe masu tasowa suna samun ci gaba cikin sauri yanzu, don haka tasirin kasashen G7 a duniya ya ragu, batun dake nufin cewa, matsayar da suka cimma ba za ta iya wakiltar ra’ayin al’ummun kasashen duniya ba. (Jamila)