logo

HAUSA

Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Gabatar Da Shawarwarin Daidaita Ci Gaban Alakar Sin Da Turai

2023-05-13 16:02:30 CMG Hausa

Dan majalissar gudanarwa, kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang, ya gabatar da shawarwari 3 na bunkasa alakar Sin da kasashen nahiyar Turai, musamman a gabar da yanayin cudanyar sassan kasa da kasa ke fuskantar sauye-sauye, da yanayi na rashin tabbas.

Qin Gang ya yi kira da a rungumi mahangar daukacin sassan duniya. Ya ce kamata ya yi Sin da Turai su martaba, da tallafawa hanyoyi mabambanta, na raya kasashe daban daban da al’ummun su suka zaba, kana su yi hadin gwiwa bisa yakini wajen daukar matakan shawo kan damuwar sassan kasa da kasa, su kare odar kasa da kasa bayan yaki, tare da rungumar manufar cudanyar dukkanin kasashe.

Kaza lika, Qin ya yi kira da a kara azamar martaba mahangar ci gaba ta tarihi. Yana mai cewa, ba abun da sassan kasa da kasa ke da buri illa samun ci gaba cikin lumana, da adalci da daidaito, da bunkasuwa, maimakon komar da hannun agogo baya.

Daga nan sai ya yi gargadin cewa, sabon salon cacar baka, ba zai haifar da komai ba sai babbar hasara, da illata moriyar al’ummun Sin da na Turai, da ma na sauran sassan duniya, kana hakan zai gurgunta manufar cudanyar kasa da kasa da tafiyar da harkokin kasa da kasa.

Bugu da kari, Qin ya kuma yi kira da a ci gaba da yin hadin gwiwa, wanda zai haifar da moriyar bai daya da cimma gajiya tare. Ya ce Sin da Turai abokan tafiya ne a fannin tunkarar barazana da kalubale, amma kuma kasar Sin na samar wa Turai da ma sauran sassan duniya kwanciyar hankali, a maimakon barazana.   (Saminu Alhassan)