logo

HAUSA

Sin ta sha alwashin bunkasa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tare da kasashen tsakiyar Asiya

2023-05-12 16:56:29 CMG Hausa

Ma’aikatar cinikayyar kasar Sin, ta ce kasar za ta yi amfani da damar taron dake tafe na Sin da kasashen tsakiyar Asiya 5, wajen aiwatar da matakan daga matsayin bunkasar hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayyar su zuwa wani sabon matsayi.

Da take tsokaci game da hakan, kakakin ma’aikatar Shu Jueting, ta ce an cimma manyan nasarori karkashin alakar hada hadar tattalin arziki tsakanin Sin da kasashen 5, wato Kazakhstan, da Kyrgyzstan, da Tajikistan, da Turkmenistan da Uzbekistan, tun bayan kafuwar dangantakar diflomasiyyarsu shekaru sama da 30 da suka gabata.

Shu Jueting, wadda ta bayyana hakan yayin taron menama labarai da aka gudanar a jiya Alhamis, ta ce darajar cinikayyar sassan ta kai dalar Amurka biliyan 70 a shekarar 2022 da ta gabata, karuwar da ta kai kaso 22 bisa dari a shekara, ya zuwa rubu’in farko na shekarar bana.  (Saminu Alhassan)