logo

HAUSA

Firaministan Jamus ya gana da Qin Gang

2023-05-11 13:09:36 CMG Hausa

Firayin ministan kasar Jamus Olaf Scholz, ya gana da mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Qin Gang a birnin Berlin, fadar mulkin kasar Jamus a jiya Laraba 10 ga wannan wata. Yayin zantawar su, Scholz ya bayyana cewa, yana sa ran za a gudanar da shawarwari tsakanin gwamnatocin kasashen biyu a karo na bakwai a kasarsa lami lafiya. Ya ce kasancewar shawarwarin na da matukar muhimmanci, yanzu haka kasar Jamus tana kokarin share fagen gudanar shi, bisa matsayinta na mai masaukin taron, tana kuma son yin kokari tare da kasar Sin wajen samun sakamako mai inganci.

A nasa bangare, Qin Gang ya bayyana cewa, a halin yanzu, ana gudanar da manyan sauye-sauye a fadin duniya, don haka ya dace sassan kasa da kasa su kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu, domin dakile kalubale tare. Haka kuma, kasashen Sin da Jamus su kara karfafa tattaunawa tsakanin su, ta yadda za su kara samar da daidaito da tabbaci ga duniya.

Qin Gang ya kara da cewa, matsayin kasar Sin kan batun Ukraine shi ne bunkasa zaman lafiya, da ingiza komawa shawarwari, kuma ya dace a tsagaita bude wuta a kan lokaci, a kuma daidaita rikicin a siyasance.

Kaza lika Qin Gang, ya ziyarci tsohon wurin kiran taron Potsdam dake karkarar Berlin, inda ya yi tsokaci da cewa, taron da aka kira a shekarar 1945, ya taka rawar gani a tafiyar da tsarin kasa da kasa, bayan yakin duniya karo na biyu, kuma hakan yana da ma’anar musamman a tarihi ga al’ummar Sinawa, ya kuma jaddada cewa, wajibi ne a kiyaye tsarin kasa da kasa bayan yakin duniya na biyu, kuma dole ne kasar Sin ta cimma burinta na dunkulewar kasa. (Jamila)