logo

HAUSA

An shirya bikin kare hakkin mata a birnin Geneva

2023-05-11 13:19:51 CMG Hausa

A jiya Laraba 10 ga watan nan ne zaunanniyar tawagar kasar Sin dake ofishin MDD na birnin Geneva na Switzerland, da sauran hukumomin kasa da kasa dake kasar, da zaunannun tawagogin kasashe masu karbar bakuncin babban taron mata na kasa da kasa, da suka hada da Mexico, da Denmark, da Kenya da sauransu, da kungiyar mata ta MDD, da kungiyar kare hakkokin bil Adam, suka shirya wani bikin hadin gwiwa mai taken “Daidaiton jinsi da hakkin mata: Ingiza ci gaban mata a sabon zamani”, a hedkwatar MDD dake Geneva, bikin da ya samu halartar wakilan da suka fito daga kasashe sama da 50.

Wakilin kasar Sin dake ofishin MDDr na Geneva Chen Xu, ya gabatar da wani jawabi yayin bikin, inda ya bayyana cewa, har yanzu akwai rashin daidaito tsakanin mata da maza a sassa daban daban na kasa da kasa, don haka kasar Sin ta yi kira da a taimakawa mata wajen kawar da talauci, ta hanyar samar musu da damammakin aiki, da kuma gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa. (Jamila)