logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Damu Da Ra’ayin EU Na Rage Barazana

2023-05-10 21:09:04 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang, ya ce kasarsa ta yaba da sanarwar da kasar Jamus da kungiyar Tarayyar Turai suka bayar, wadda ke cewa ba sa neman janye jiki daga kasar Sin, amma kuma kasar Sin ta damu da  da EU ke yi dangane da batun rage barazana.

Qin Gang wanda ke ziyara a kasar Jamus, ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai da ya yi tare da ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock, bayan tattaunawarsu a Berlin.

Acewarsa, kasar Sin ba ta kakabawa kasashen waje tsarin ta, kuma ta kasance mai nacewa ga bin hanyar zaman lafiya da inganta manufar bude kofa bisa moriyar juna. Haka kuma ta na kiyayewa tare da daukaka tsarin kasa da kasa bisa dokoki, da adawa da babakere da danniya da cin zali, yana mai cewa, kasar Sin ba za ta taba aiwatar da wani abu kamar na fasa bututan iskar gas na Nord Stream ba.

Ya kara da cewa, abun da kasar Sin ke gabatarwa ga kasashen waje shi ne, damarmaki ba rikici ba, da hadin gwiwa maimakon fito-na-fito, da zaman lafiya maimakon tashin hankali, da kuma tabbaci maimakon barazana.

Bugu da kari, Qin Gang ya ce idan wasu kasashe ko bangarori na neman rage tasirin kasar Sin da sunan rage barazana, to kuwa za su yi hannun riga da damarmaki da hadin gwiwa da zaman lafiya da ma ci gaba.

Ya ce dole ne a tsaya tsayin daka wajen adawa da rabuwar kai da haifar da tsaiko ga tsarin samar da kayayyaki, a kuma sa ido sosai don yaki da sabon yakin cacar baka da hada hannu wajen tabbatar da tsarin samar da kayayyaki na duniya mai karko da aminci. (Fa'iza)