logo

HAUSA

Qin Gang ya tattauna da takwararsa ta Jamus

2023-05-10 13:41:52 CMG Hausa

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Qin Gang ya yi shawarwari da takwararsa ta kasar Jamus Annalena Baerbock a birnin Berlin, fadar mulkin kasar Jamus a jiya Talata 9 ga wannan wata, agogon wurin.

Yayin shawarwarin, Qin Gang ya bayyana cewa, Sin da Jamus, manyan kasashe ne dake jawo tasiri a duniya, ya dace su kara karfafa tattaunawa da hadin gwiwa dake tsakaninsu, kuma kamata ya yi su nace kan manufar adalci, su yi adawa da sabon yakin cacar baka, da ra’ayin ware kai, ta yadda za su kara kuzari kan zaman lafiya da wadata a duniya.

A nata bangare, Baerbock ta yi tsokaci cewa, kasarta ta Jamus tana mai da hankali matuka kan cudanyar manyan jami’ai da hadin gwiwa dake tsakanin sassan biyu, kuma tana fatan za a gudanar da tattaunawa tsakanin gwamnatocin kasashen biyu karo na bakwai yadda ya kamata.

Kazalika, sassan biyu sun yi musayar ra’ayi kan batun Ukraine. Qin Gang ya yi bayani kan ra’ayin kasar Sin kan batun, inda ya jaddada cewa, matsayin kasar Sin a ko da yaushe shi ne bunkasa zaman lafiya, da ingiza komawa shawarwari, kuma ya dace kasashen Turai su yi kokari tare domin maida zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar ta Ukraine. (Jamila)