logo

HAUSA

Sin na fatan za a kauce tasirin rikicin Sudan kan batun Abyei

2023-05-10 13:49:01 CMG Hausa

Zaunannen mataimakin wakilin kasar Sin dake MDD Dai Bing ya yi tsokaci yayin taron da kwamitin sulhun majalisar ya kira domin tattauna kan yanayin da yankin Abyei ke ciki jiya Talata 9 ga wannan wata da cewa, kasar Sin tana fatan rikicin kasar Sudan ba zai jawo mummunan tasiri kan batun yankin, kuma tana fatan bangarorin da abin ya shafa za su ci gaba da yin kokari domin tabbatar da matsayin yankin Abyei yadda ya kamata.

Dai Bing ya kara da cewa, a makonnin baya bayan nan, shugabannin kasashen Sudan da Sudan ta kudu sun taba bayyana cewa za su yi kokari domin daidaita batun game da matsayin yankin Abyei, amma abun bakin ciki shi ne Sudan ta shiga yanayin tangarda yanzu, don kasar Sin tana fatan Sudan za ta tsagaita bude wuta a kan lokaci, kuma ta hakake cewa, Sudan da Sudan ta kudu za su ci gaba da yin shawarwari da hadin gwiwa, ta yadda za su tabbatar da matsayar guda da suka cimma.

Kazalika, ya nuna cewa, kasar Sin ta yaba da kokarin da rundunar sojojin MDD dake yankin Abyei take yi domin tabbatar da tsaro a yankin, kuma za ta ci gaba da goyon bayan aikin rundunar sojojin ta hanyar daukar hakikanin matakai, ta yadda za ta taka rawar gani wajen kiyaye tsaro a yankin. (Jamila)