logo

HAUSA

Bunkasar Cinikin Waje Ta Kasar Sin Ta Wuce Zaton Mutane

2023-05-09 21:53:58 CMG Hausa

Hukumar kwastam ta kasar Sin ta bayyana yau Talata cewa, darajar kayayyakin da kasar ta sayar zuwa ketare a watan Afrilun bana ta kai kudin Sin RMB yuan traliyan 2.02, wadda ta karu da 16.8% bisa na makamancin lokacin bara. Bunkasar darajar kayayyakin da kasar Sin ta sayar zuwa ketare a watan Afrilu ta sake wuce zaton mutane. Kamfanin dillancin labaru na AP ya ruwaito cewa, ko da yake bukatun da ke akwai a duniya sun yi rauni, amma kasar Sin ta yi fice wajen sayar da kaya zuwa ketare.

Me ya sa hakan? Saboda gwamnatin kasar Sin ta dade tana kara azama kan manufarta ta bude kofarta ga ketare, da fitar da matakan tabbatar da kwanciyar hankali a cinikin waje. Tun daga farkon shekarar bana ne hukumomin sassan kasar Sin suka dauki matakan sa kaimi kan bunkasuwar cinikin waje, kana kamfanonin kasar Sin sun je ketare domin neman kwangiloli. A karshen watan Afrilu kuma, gwamnatin Sin ta fitar da wasu sabbin matakai, ciki had da maido da shirya shagulgula a zahiri a gida, shirya tattaunawa tsakanin kamfanonin kera motoci da kamfanonin jigilar kaya cikin jiragen ruwa, da goyon bayan kamfanonin cinikin waje su yi ciniki ta yanar gizo tsakanin kasa da kasa da kuma habaka hanyoyin sayar da kayayyaki. Dukkan matakan suna da amfani da dacewa, tare da samarwa kamfanonin cinikin waje sabbin damammakin ci gaba.

An yi imanin cewa, sakamakon gudanar da shagulgula da dama a gida, da kara saukaka yin mu’amala a tsakanin mutane, da kuma rika yin kirkire-kirkire a harkokin ciniki, kasar Sin za ta samu karin kuzari kan raya cinikin waje, kuma za ta kara aikewa duniya alamar saurin farfadowar tattalin arzikinta. (Tasallah Yuan)