logo

HAUSA

AL za ta kafa tawagar cudanya ta ministoci domin dakile rikicin Sudan

2023-05-08 14:48:56 CMG Hausa

Hukumar kungiyar kasashen Larabawa wato AL ta zartas da kuduri jiya Lahadi cewa, za ta kafa tawagar cudanya ta ministoci domin tattaunawa da bangarori daban daban na kasar Sudan da wasu kasashe masu ruwa da tsaki, ta yadda za a daidaita rikicin Sudan yadda ya kamata.

An kira taron musamman na hukumar AL karkashin jagorancin kasashen Masar da Saudiyya a birnin Alkahira, fadar mulkin kasar Masar jiya, inda ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa suka tattauna kan rikicin da ake gwabzawa a kasar Sudan, kana suka zartas da kudurin domin neman samun dabarun daidaita rikicin cikin lumana.

Bayan taron, kungiyar AL ta fitar da sanarwa, inda ta bayyana cewa, tawagar za ta hada wakilan da za su fito daga kasashen Saudiyya da Masar da kungiyar AL da sauransu. Kuma tawagar za ta tattauna da bangarori daban daban na Sudan da wasu kasashe masu ruwa da tsaki domin tabbatar da tsagaita bude wuta daga duk fannoni a kasar ta Sudan, ta yadda za a daidaita rikicin kasar cikin lumana bisa bukatar zaman lafiya da kwanciyar hankali ta al’ummar kasar. (Jamila)